BOKO HARAM TA LALATA MAKARANTU SAMA DA 5,000 A BORNO
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce rikicin Boko Haram ya lalata gine-ginen makarantu sama da 5,000 tare da hana yara kimanin miliyan 2.2 zuwa makaranta a lokacin da rikicin ya tsananta.
Zulum ya bayyana hakan ne a Maiduguri, inda ya ce rikicin ya kuma yi sanadin mutuwar malamai da masu kula da makarantu da dama.
Ya ce gwamnatin Borno ta kashe sama da Naira biliyan 46 kan ilimin firamare da sakandare a shekarun kasafin kuɗi na 2025 da 2026.
A cewarsa, an kammala ayyukan ilimi 136, yayin da yawan ɗaliban da ke zuwa makaranta ya ƙaru daga 766,551 a 2019 zuwa 1,801,295 a 2026.
Gwamnan ya ce matakan na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na farfaɗo da harkar ilimi da samar wa yara kyakkyawar makoma.
