Jerin sunayen, wanda sakatariyar hukumar Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu, ya ƙunshi ƴan takara daga jam’iyyun siyasa 18 da za su fafata neman shugabancin Najeriya.
Kamfanin Dillancin Labaran ƙasar NAN, ya ruwaito cewa cikin ƴan takarar shugaban ƙasa 18, akwai maza 16 ne yayin da ake da mata biyu ne kacal.
Daga cikin ƴan takarar maza akwai Bola Tinubu na jam’iyyar APC, Abubakar Atiku na ADC, da Peter Obi na NDC.
Sauran sun haɗa da Adewole Adebayo na SDP, Oluseyi Makinde na APM, Donald Duke na PRP, Chibuzor Okereke na Labour Party, LP, da Omoyele Sowore na AAC.
Ƴan takarar mata biyu da ke cikin jerin sunayen kuwa su ne Okwori Fredrick ta jam’iyyar NDP, da Dakta Esther Okereke ta NRM.
