Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya yi zargin cewa wasu mutane da ba a ambaci sunansu ba suna neman wata hanya ta kawar da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
A cikin wani bidiyo da aka wallafa a X, Ayodele ya gargadi ‘yan siyasar biyu da su kula da tsaronsu.
Duk da cewa bai ambaci sunayen wadanda ya yi zargin suna shirin kawar da Obi da Atiku ba, malamin ya ce Allah ba zai bari hakan ta faru ba.
“Obi da Atiku, ku kula da tsaronku sosai. Suna neman duk wata hanyar kawar da Obi da Atiku.”
“Amma Allah ba zai taɓa barin hakan ta faru ba. Ku yi hattara ku yi taka tsantsan da tsaronku,” in ji shi.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa yayin da Atiku shine ɗan takarar shugaban ƙasa na African Democratic Congress, ADC, Peter Obi shine ɗan takarar Nigerian Democratic Congress, NDC, kafin zaɓen 2027.
Limamin ya kuma yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da kada ya ziyarci Amurka, yana mai zargin cewa Amurka ta kusa durƙushewa.
