Attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ya fi son a saka shi a gidan yari maimakon a ƙwace masa wayarsa, yana mai cewa rasa damar amfani da ita ba abin da zai amince da shi ba ne.
Dangote ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Legas, inda ya ƙaddamar da shirin “Vision 2030” na bunƙasa masana’antu a Afirka.
An tambaye shi ko zai fi son ya yi mako guda ba tare da wayarsa ba ko kuma ya rasa damar amfani da jirginsa na kashin kansa.
Da yake amsa tambayar, Dangote ya ce zai fi masa sauƙi a ɗaure shi fiye da a ƙwace masa waya.
Attajirin ya kuma bayyana cewa yana da lambobin waya sama da 13,000 a cikin wayarsa, yana mai cewa hakan na taimaka masa wajen hulɗa da mutane a ɓangarorin rayuwarsa da kasuwancinsa.
Ya ce ba ya yawan goge lambobin mutane, lamarin da ya taimaka wajen yawan lambobin da ke cikin wayarsa.
Dangote shi ne shugaban rukunin kamfanonin Dangote Group, wanda ke da manyan masana’antu da harkokin kasuwanci da suka haɗa da siminti, taki, matatar mai da sauran fannoni a faɗin Afirka.
