Hukumar ta bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin yin katsalandan a ƙuri’un jama’a zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin kurkuku da kuma biyan tara, bisa tanadin dokokin zaɓe.
Wannan gargaɗi na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027, wanda ake sa ran zai kasance mai muhimmanci ga makomar siyasar Najeriya.
INEC ta jaddada muhimmancin gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, domin tabbatar da cewa ƙuri’un jama’a ne za su tantance waɗanda za su jagorance su.
