APC ta janye ƙarar da ta shigar kan zaɓen Adeleke
Jam’iyyar APC ta janye ƙarar da ta shigar tana kalubalantar nasarar Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a zaɓen gwamna na ranar 15 ga Agusta, 2026.
Lauyan da ya shigar da ƙarar, Oluseyi Oyagbile, ya tabbatar da cewa ya janye ta ne a ranar Talata bayan samun sabon umarni daga wanda yake wakilta da shugabannin jam’iyyar APC.
A baya, tawagar lauyoyin APC ta bayyana cewa jam’iyyar da ɗan takararta, Bola Oyebamiji, ba su amince da shigar da ƙarar ba, musamman bayan Oyebamiji ya amince da shan kaye tare da taya Adeleke murna.
Hukumar INEC ta bayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kuri’u 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu kuri’u 444,815.
Da janye ƙarar APC, ƙalubalen shari’a kan nasarar Adeleke yanzu ya rage ga wata ƙara daban da aka shigar a madadin jam’iyyar PDP, wadda ita ma ta haifar da ce-ce-ku-ce kan sahihancin izinin shigar da ita.
See less
