Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma dan takarar jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan rahotannin cewa wasu matasan Najeriya na sayar da kodarsu domin samun kudin da za su rayu.
Atiku, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ya danganta lamarin da tsadar rayuwa da manufofin tattalin arziki na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ya ce matasa ya kamata su rika sayar da dabaru, kirkire-kirkire da hazakarsu, ba sassan jikinsu ba. Ya kuma yi ikirarin cewa wasu na sayar da koda kan kusan Naira miliyan 1.7.
Atiku ya ce tsadar abinci, sufuri, haya, kudin makaranta, magunguna da wutar lantarki na kara jefa jama’a cikin matsanancin hali.
Ya kuma bukaci gwamnati ta aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da za su rage wahalhalun jama’a, tare da samar da abinci mai saukin kudi, ayyukan yi da ingantaccen tsarin kiwon lafiya.
Ya ce duk da cewa akwai dokokin da suka haramta cinikin gabobin jiki, dokoki kadai ba za su magance talauci da matsananciyar rayuwa da ke sa matasa fadawa hannun masu safarar gabobin jiki ba.
Atiku ya karkare da cewa: “Tinubu ya mayar da Najeriya mai tsada, ni kuma zan mayar da Najeriya mai saukin rayuwa.”
